Connect with us

News

Ilimi ya samu kaso mafi tsoka yayin da Ganduje ya gabatar da N245bn kasafin-kuɗi na 2023 ga Majalisa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da kasafin kudi na Naira biliyan 245 na shekarar 2023 ga majalisar dokokin jihar domin amincewa.

 

Advertisement

Da ya ke gabatar da kasafin a yau Juma’a a Kano, Ganduje ya ce an sanya wa kasafin kuɗin, mai taken kasafi na ci-gaba da wadata II, da nufin karfafawa tare da inganta rayuwar al’ummar jihar.

Gwamnoni uku na shirin halasta kuɗin haram a Najeriya – EFCC

Advertisement

Ya ce kasafin ya kunshi manyan ayyuka da za a kashe Naira biliyan 144, wanda ya nuna kashi 59 cikin 100 da kuma Naira biliyan 100 da za a kashe a harkokin yau da kullum, wanda ya nuna kashi 41 cikin 100.

 

Advertisement

Gwamnan ya ce bangaren ilimi shi ne ya fi ɗaukar kaso mafi tsoka, inda a ka ware masa Naira biliyan 62, wanda ya nuna kashi 27 cikin 100 fiye da adadin da UNESCO da Majalisar Dinkin Duniya suka ba da shawarar a rika fitar wa, inda ya ce za a fitar da kudaden ne wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsare da nufin tabbatar da ingantaccen ilimi a dukkan matakai.

 

Advertisement

Ya ce za a kuma yi amfani da wani bangare na kudaden wajen inganta shirin ilimi kyauta kuma dole a jihar.

 

Advertisement

Ganduje ya ce an ware wa fannin lafiya Naira biliyan 39.1, albarkatun ruwa Naira biliyan 15, ɓangaren sufuri Naira biliyan 8.6, fannin noma Naira biliyan 19.9 da ayyuka da kayayyakin more rayuwa Naira biliyan 35.

 

Advertisement

Ya bukaci ‘yan majalisar su tabbatar da gaggauta amincewa da kasafin kudin domin baiwa gwamnati damar ci gaba da samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar.

 

Advertisement

Gwamnan ya kuma bukaci matasa da su guji duk wani tashin hankali musamman ganin zaben 2023 ya kara kusanto.

 

Advertisement

A nasa jawabin shugaban majalisar, Alhaji Hamisu Chidari, ya baiwa gwamnan tabbacin yin gaggawar zartar da kasafin kudin domin samun damar darewa kan kasafin kudin watan Janairu zuwa Disamba.

 

Advertisement

Chidari ya bukaci Ma’aikatun Gwamnati da Hukumomi (MDAs) da su kasance a shirye don kare kasafin kudi a majalisar.

 

Advertisement

Kakakin majalisar ya kuma yaba wa gwamnan bisa kokarin da ya ke yi a bangaren samar da ababen more rayuwa, tsaro, lafiya da ilimi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending