News
Sojoji Sun Kashe Babban Dan Boko Haram Sun Cafke 27
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Sojoji sun kashe shahararren dan ta’addan Boko Haram, Lawan Yashin, tare da cafke wani dauke katunan zabe 67 a sananin gudun hijira a Jihar Borno.
Hedikwatar Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) da hadin gwiwar dakarun CJTF ta ce a ranar Alhamis ne suka kashe Lawan Yashin tare kuma da kama wani Burama Modu dauke da katin zabe 67 na dindindin a Maiduguri.
Gwamnoni uku na shirin halasta kuɗin haram a Najeriya – EFCC
Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo-Janar Danmadami Musa, ya ce an kashe Lawan Yashin ne a lokacin da yake kokarin tserewa bayan ya ga sojoji tare da wasu 19 daga abokan ta’addancinsa a sansanin ’yan gudun hijira da ke Shuwari a Karamar Hukumar Maiduguri.
Manjo-Janar Danmadami Musa ya kara da cewa kana an kuma kama mutane 27 da ake zargin ’yan Boko Haram/ISWAP ne da kwato makamai da alburusai da daman gaske a hannunsu.
Ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin da katunan zaben ne a sansanin ’yan gudun hijira da ke Shuwari kuma yana hannun sojoji domin amsa tambayoyi.
Ya yi wannan bayani ne a taron ’yan jarida kan sabbin ayyukan Rundunar Sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro kan magance kalubalen tsaro tsakanin ranakun 20 ga Oktoba zuwa 3 ga watan Nuwamba,2022.
A cewarsa, hare-haren da dakarun tsaron ke kaiwa sun yi nasarar kashe ’yan ta’adda da dama da kuma kwace manyan motoci masu dauke da bindigogi guda bakwai da sauran kayayyakin yaki mallakar’ yan ta’addar.
“Hakazalika, bisa sahihin bayanan sirri na ’yan ta’addan da ke yin sintiri a yankunan Abulum da Njibul da ke kusa da dajin Sambisa, rundunar ta kai farmaki a wuraren a lokaci guda tare da kashe ’yan ta’adda da dama, yayin da aka ga wadanda suka ji rauni sun ranta a na kare,” in ji shi.
Janar Danmadami ya kuma bayyana cewa, a tsawon lokacin ’yan ta’addan Boko Haram 145 da iyalansu, maza 30, mata 33 da kananan yara 82 ne suka mika wuya ga sojoji a wurare daban-daban a Arewa maso Gabas.”
Babban kwamandan sojojin ya yaba wa kokarin da sojojin ke yi a bangarori daban-daban a fadin Najeriya .
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
