News
Kotu Ta Baiwa EFCC Damar Gwanjon Wasu Kadarorin Ekweremadu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Yaki da masu yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a yau Juma’a ta samu amincewar wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, kan kwace wasu kadarori na wucin gadi 40 mallakar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sen. Ike Ekweremadu.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar da wannan umarni ne a lokacin da yake yanke hukunci kan karar da EFCC ta shigar a kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1242/2022.
KODA ZAN YARDA AYI SULHU SAI YA TARA YAN JARIDA YA KARYATA KAN SA~Hadiza Gabon
Hukumar ta garzaya kotu domin ta ba da umarnin kwace kadarorin wadanda binciken hukumar suka tabbatar da ya mallaki wadannan kadarori ba bisa ka’ida ba.
Hukumar EFCC din ta ce kudin da aka mallaki Kadarorin tana kyautata zaton an same su ne ta haramtacciyar hanya.
Har ila yau, ta kara da cewa akwai bukatar ayi Gwanjon Kadarorin, don tseratar da su daga lalacewa.
Wannan mataki na karkashin Sashe na 17 na Dokar hana zamba da sauran Laifukan da suka danganci zamba ta 2006.
A wani takaitaccen hukunci da ya yanke kan karar, Alkalin ya amince da bukatar, inda ya umurci hukumar EFCC da ta yi Gwanjon Kadarorin ta hanyar wallafa su yadda duniya zata gani, domin samun damar siyar da su.
Daily Nigerian ta rawaito cewa odar kwace kadarorin ta wucin gadi za a aiwatar da ita ne, a kowace rana cikin kwanaki bakwai daga ranar da aka bayar da odar.
Mai shari’a Ekwo ya dage sauraron karar har zuwa ranar 5 ga Disamba, 2022, domin samun rahoto na musamman.
Afeez Mustapha, wani mai bincike a hukumar EFCC, a wata takardar goyon bayan amincewa da bukatar, ya bayyana cewa hukumar ta fara binciken Ekeremadu ne biyo bayan wasu bayanan sirri da ta samu daga wasu kasashen waje bisa zargin karkatar da kudade da suka hada da mallakar wasu kadarori a Birtaniya, Dubai da kuma Amurka ta hanyar wakilai da kamfanoni marasa rijista.
Jadawalin kadarorin da Ekweremudu ya mallaka tare da wasu kudade da har da wani gida dake a Landan Flat 4, Kotun Varsity, Hormer Street.
Kaddarori uku a Florida, dake Amurka, daya daga cikin wanda aka saya akan dalar Amurka $155,000; wata kadara da ke kan fili mai fadin murabba’in mita 3000 mai dauke da dakuna 7 masu dauke da Boys Quarters, wurin wanka, garejin mota guda 3 tare da kofofin rufewa, gidan mai garejin ne kuma, da sauran su.
