Connect with us

News

Yan bindiga sun kashe mutum 18 a Benue

Published

on

Yan bindiga

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

Akalla mutum 18 suka rasa rayukansu bayan hari da ‘yan bindiga suka kai hari a yankin Ukohol na karamar hukumar Guma da ke jihar Benue.

 

Advertisement

Jaridar Daily Trust  ta ruwaito cewa mai bai wa shugaban karamar hukumar shawara kan harkar tsaro Christopher Waku, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin jiya Alhamis lokacin da mutane suke tsaka da cin kasuwa a yankin.

COP 27: Ambaliyar Ruwa A Najeriya, Da Wasu Ya Zama Wani Bangare Na Abun Tattaunaw

Ya kuma ce ana ci gaba da bincike domin gano wadanda suka bata.

 

Shi ma, shugaban karamar hukumar, Mike Ubah, ya tabattarwa manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan bindigar sun zo ne sanye da baƙaken kaya, inda da isar su suka fara buɗewa mutane wuta a cikin kasuwar da kashe goma nan take.

 

Advertisement

Ubah ya kara da cewa sun kai wasu hare-hare a kauyuka da ke kusa tare da kashe mutum takwas.

 

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta tabbatar da kai harin amma ta ce ba su da wasu bayanai ya zuwa yanzu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending