News
Kwankwaso ba kashin yarwa bane, Rigima da Murtala Garo Yanzu Aka Fara – Alhassan Doguwa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta tarayya Alhassan Ado Doguwa ya ce Kwankwaso ba abin yarwa bane a Kano.
A cewarsa in dai mutum zai fadi tsakani da Allah ya san cewa Kwankwaso a matsayin sa na gwamnan, yayi aikin da kowa ya yaba.
KODA ZAN YARDA AYI SULHU SAI YA TARA YAN JARIDA YA KARYATA KAN SA~Hadiza Gabon
A jawabin da ya gabatar ga magoya bayansa a daren yau Juma’a Doguwa ya ce, Duk Ɗan Kano ƙarya yake yace Kwankwaso bai yi rana ba.
Doguwan ya kuma yi zazzafan martani ga mataimakin Ɗan Takarar Gwamnan Jam’iyyar APC a Kano Alhaji Murtala Sule Garo.
A cewar shugaban masu rinjayen ba za su yi shi ba, kuma rigima tsakaninsa da Murtala yanzu a ka soma.
Alhassan Ado Doguwa ya zargi Murtala Sule Garo bai kammala makarantar sakandare ba, sannan ya zargi bai kammala jami’a ba, amma zai ɗauki lauyoyi don yin cikakken bincike don kada a yi kitso da ƙwarƙwata.
Alhassan Ado ya yi wannan zargi ne lokacin da yake yiwa magoya bayansa jawabin halin da ake ciki a jam’iyyar APC, biyo bayan shata layi tsakani.
