News
COP 27: Ambaliyar Ruwa A Najeriya, Da Wasu Ya Zama Wani Bangare Na Abun Tattaunaw
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Asara da barnar da aka samu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a Najeriya da Pakistan da sauran wasu kasashen Afirka masu tasowa za su kasance cikin ajandar taron COP 27.
Ambasada Wael Aboulmagd, mai ba da shawara na musamman ga zababben shugaban COP, ya bayyana hakan a ranar Juma’ar nan yayin wani taron manema labarai na zahiri a shirye-shiryen taron sauyin yanayi na duniya.
KODA ZAN YARDA AYI SULHU SAI YA TARA YAN JARIDA YA KARYATA KAN SA~Hadiza Gabon
Taron COP 27 shi ne yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na shekarar 2022, UNFCCC, wadda aka shirya gudanarwa a birnin Sharm El Sheikh na kasar Masar tsakanin ranar 6 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Nuwamba.
Mista Aboulmagd ya ce akwai bukatar a yi shiri don taimakawa wadanda bala’in sauyin yanayi ya shafa a kasashen.
“Baya ga ajanda kan rage sauyin yanayi da daidaitawa, za mu kuma tattauna asara da barnar da aka samu.
“Muna sane da yadda ambaliyar ruwa ke shafar mutane a Pakistan, Najeriya da wasu kasashen yammacin Afirka.
“Dole ne mu nemo tsari na ƙarshe don taimaka wa mutane a waɗannan ƙasashe. Ina ganin muna da dukkan damar da za mu tattauna hakan,” inji shi.
Mashawarcin na musamman ya ce fadar shugaban kasa ta ji dadin yadda aka yi rajistar COP 27, inda ya ce a yanzu kowa ya san girman halin da ake ciki.
Jaridar DailyNigerian ta rawaito cewa, Mista Aboulmagd ya bukaci dukkan mahalarta taron da su tunkari taron da karfin gwiwa yana mai cewa lokaci ya canza kuma ana bukatar shigar da adalci a cikin duniya.
