Business
Kamfanin Meta mai mallakin Facebook zai kori ma’aikata 11,000
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kamfanin Meta mai mallakin shafukan Facebook da Instagram da kuma WhatsApp, ya bayyana cewa zai rage kashi 13 cikin 100 na ma’aikatansa.
Abin da ke nufin kamfanin zai kori ma’aikata 11.000 daga cikin ma’aikatansa 87,000 a fadin duniya.
Sadio Mane ya ji rauni a wasan da Bayern ta Lallasa Weder Bremen
A wata sanarwa da shugaban kamfanin Mark Zuckerberg ya fitar, ya ce rage ma’aikatan na daga cikin wasu sauye-sauye masu tsanani da kamfanin ya gudanar a tarihinsa.
BBC ta rawaito cewa Shi ma dai kamfanin Twitter ya bayyana rage rabin ma’aikatansa.
Advertisements
