News
Ɗan shekara takwas ya mutu bayan shafe kwana uku a rijiya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wani yaro ɗan shekara takwas a Indiya ya rasa ransa, bayan fada wa cikin rijiya kwanaki uku da suka gabata.
Yaron mai suna Tanmay Sahu, ya fada cikin rijiyar ne da ke garin Madhya Pradesh lokacin da yake wasa da abokansa a yammacin ranar Talata.
An yanke wa attajiri Jimmy Lai hukuncin daurin kusan shekaru 6 a gidan yari
An aike da jami’an ceto zuwa wurin tun bayan faruwar lamarin da nufin fitar da yaron, sai dai sun same shi ba ya numfashi lokacin da suka kai kasan rijiyar mai zurfin kafa 55 zuwa 400.
Daga nan aka garzaya da shi zuwa asibiti, inda kuma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Advertisements
