Connect with us

News

Yan sandan Jamus sun gano kayan tarihin da aka sace na dala miliyan 119

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

‘Yan sanda a Jamus sun ce sun gano wasu daga cikin muhimman kayayyakin tarihi da aka sace daga wani gidan sarauta da ke birnin Dresden shekara uku da suka wuce.

 

Advertisement

Daga cikinsu, an dawo da kaya 31 inda aka kai su gidan adana kayan tarihi na Green Vault.

Gwamnatin Najeriya na fatan haɓaka hada-hadar cikin ƙasa zuwa dala tiriliyan 12

Daga cikin kayan akwai wata tauraruwa ta lu’u lu’u da ake maƙalawa a jikin kayan sarauta da kuma wani bindin tsuntsu da aka yi wa kwalliyar zinare da ake makalawa a jikin kayan sarautar.

 

Mahukuntan kasar sun ce an gano kayan ne bayan tattaunawa da lauyoyin wasu mutum shida da ake yi wa shari’a a kan sace kayan.

 

BBC ta rawaito cewa Masu shigar da karar sun ce darajar kayan da aka sace ta kai dala miliyan 119.

Advertisement

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending