Connect with us

News

Yan bindiga sun kwashe mazajen wani kauye dake Zamfara

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

‘Yan bindiga a Najeriya sun kwashe daukacin mazajen garin Randa dake karamar hukumar Maru a Jihar Zamfara saboda bacewar bindigoginsu, yayin da suka yi sanadiyar mutuwar 20 daga cikin su.

 

Advertisement

Rahotanni sun ce mabiya wani gawartaccen ‘dan bindigar yankin da ake kira Lawali Damina ne suka aikata wannan aika aikan na kwashe mazajen wannan gari, cikinsu harda kananan yara saboda bacewar bindigogin mabiyansa guda 2.

 

Advertisement

Sabbin Takardun Kudin Da CBN Ya Fitar Sun Kare Tatas A Bankuna

 

 

Advertisement

Bayanai sun ce wadannan bindigogi guda biyu sun bace ne lokacin da akayi arangama tsakanin magoyan bayan Damina da wasu abokan gabarsu akan wata budurwa.

 

Advertisement

Jaridar Premium Times ta jiyo daga mazauna yankin dake kan iyakar jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Kebbi, inda Yan bindiga ke cin karensu babu babbaka abinda ya faru dangane da kwashe mutanen.

 

Advertisement

A wannan yanki ne ‘yan bindiga ke sanya haraji da kuma gindaya sharidodi ga jama’a akan yadda zasu gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Basaraken Mutumji dake kula da kauyen Randa, Abdulkadir Abdullahi ya shaidawa jaridar cewar tuni kauyen ya biya kudin kariyar da’ yan bindigar suka bukata a karkashin Damina domin kaucewa kai musu hari.

Advertisement

 

Bayanai sun ce a makon jiya ne aka fafata tsakanin mabiyan Damina da na abokan adawarsu akan wata budurwa da ta ziyarci yankin daga Shinkafi, abinda ya kaiga kashe wasu daga cikinsu da kuma bacewar makamansu.

Advertisement

 

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Advertisement

 

Basaraken yace wannan ne dalilin da ya sa Damina ya ziyarci garin, inda ya bukaci yiwa mabiyansa jana’iza da kuma neman bindigogin da suka mallaka.

Advertisement

 

Rahotanni sun ce rashin ganin bindigogin ya sa ya tafi da mutane 270 maza da suka hada da manya da kuma kananan yara.

Advertisement

 

Basaraken yace sun shaidawa jami’an gwamnati halin da ake ciki amma babu wanda ya kai musu dauki.

Advertisement

 

Ya zuwa wannan lokaci babu wani martani daga gwamnatin jihar Zamfara akan lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending