Connect with us

News

Adadin mutanen da dusar kankara ta halaka a Amurka ya zarce 50

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

Guguwar dusar kankarar kashe mutane da dama a Amurka a karshen mako yayin bikin Kirsimeti na ci gaba mamaye jihar New York tare da katse hanzarin dubban fasinjojin jiragen sama a fadin kasar.

 

Advertisement

 

 

Adadin mutanen da suka mutu yayin guguwar ta hunturun, wadanda galibinsu suka rasa rayukansu a kan hanyoyi manya da kanana ya haura 50, bayan da jami’ai suka tabbatar da sake samun asarar rayuka a gundumar Erie da ke yammacin jihar New York inda iftila’in yafi tsanani.

MAKARANTAR AL’MADINA TAHAFIZUL QUR’AN DAWAKIN TOFA TA GUDANAR DA SAUKAR KARATUN AL’QUR’ANI MAI GIRMA

Wani Karin tashin hankali da ake ciki, shi ne fargabar da ake na ganin karuwar adadin mutanen da tsananin sanyin ke halakawa, kamar yadda Byron Brown, magajin garin Buffalo dake jihar ta New York, yankin da yafi fuskantar iftila’in da ya katse wutar lantarkin dubban mutane.

 

Yadda dusar kankara ta rutsa da mutane cikin motocinsu a Amurka.

Advertisement

Yadda dusar kankara ta rutsa da mutane cikin motocinsu a Amurka. AP – Neil Blake

Yayin da yanayin sanyin ya tsananta, matafiya da wasu mazauna da ke tserewa daga gidajensu masu daskarewa sun makale a kan manyan hanyoyi, abin da ya sanya aka gaza ceto su daga halaka.

 

 

TALLA

 

Advertisement

Iyalan wata mai shekaru 22 da ke zaune a garin Buffalo, Anndel Taylor, sun ce matashiyar ta mutu a cikin motarta bayan da ta makale a kan hanyarta ta komawa gida daga wajen aiki.

 

Bidiyon da Taylor ta aika kuma ‘yar uwarta ta watsa a intanet nuna yadda motarta ta nutse cikin dusar kankara har zuwa tagogint.

 

Masu ba da agajin gaggawa, wadanda suma da kansu sai da makale suna kokarin ceto ta, sun samu nasarar ciro gawarta daga motar ne bayan sa’o’i 18.

 

Advertisement

Wani magidanci ma ya shaidawa jaridar New York Times cewa, sai da ya shafe sa’o’i 11 makale cikin motarsa tare da kananan yaransa 4, kafin daga bisani jami’an agaji su ceto su.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending