Connect with us

News

DSS Ta Cafke Mutum 2 Kan Zargin Tayar Da Bam Yayin Ziyarar Buhari Jihar Kogi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

 

 

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da tayar da bam a Mota a ranar 29 ga Disamba, 2022, kusa da fadar Ohinoyi na Ebiraland a Okene, jihar Kogi.

 

Advertisement

 

 

Ku tuna cewa fashewar ta faru ne jim kadan gabanin ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin kaddamar da wasu ayyuka a jihar

Mutum goma sun rasu a hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi

Wadanda ake zargin dai sun hada da Abdulmumin Ibrahim Otaru wanda akafi sani da Abu Mikdad da kuma daya daga cikin abokansa, Saidu Suleiman.

 

 

Advertisement

Mai magana da yawun hukumar DSS, Dr. Peter Afunanya, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar 3 ga watan Janairun 2023, kuma Otaru ya samu rauni a kafarsa ta hagu yayin da yake kokarin tserewa.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending