News
Yarima Munir Ja’afaru, Ya Miƙa Takardar Murabus ɗinsa na Hakimin Basawa.
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Munir Ja’afaru, Wanda aka fi sani da Madakin Zazzau, Ya sauka daga Mukaminsa ne bayan da ake zargin anyi masa katsalandan a kan zaɓen Shugaban unguwa.
An ruwaito cewa, Sarki Jaafaru dan Isyaku, mahaifinsa, Yayi sarauta Daga 1937 zuwa 1959, kuma Munir Ja’afaru ya kasance mai fafutukar neman Sarautar bayan rasuwar Sarki Shehu Idris a watan Satumban 2020.
Ranar Yaki Da Cizon Sauro: Majalisa Ta Bukaci Gwamnati Ta Ayyana Dokar Ta-baci Kan Malaria
Majiyoyi Daga masarautar sun bayyana cewa hakimin ya yanke shawarar yin murabus ne biyo bayan kin Amincewa da naɗin da Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli y yi masa na Naɗin Unguwar Gwaba.
A al’adar Zazzau, hakimin Gundumar ne ke naɗa masu unguwanni, Sannan a Hukumance aka yi musu ado da rawani a dakin taro na fadar sarki (Zaure) Sannan kuma magatakardar Hakimin (Magatakarda) ya mika wa sarki don Amincewa.
Sai dai wani batu ya taso a lokacin da aka Gabatar da sabon hakimin Unguwar Gwaba da akayi wa ado ga sarki Domin amincewa. Sarkin yayi tambaya kan rashin Zuwan hakimin, Nan take ya ba da umarnin a cire rawani na hakimin.
Kakakin Masarautar Zariya Abdullahi Aliyu ya tabbatar da murabus ɗin ta hanyar wata sanarwa. Koda yake bai yi ƙarin haske kan dalilan yin murabus ɗin ba, ya nuna cewa Sarkin ya Amince da Murabus din tare da bayyana wanda zai maye Gurbinsa.
Ya cigaba da cewa, “Bayan samun takarda mai kwanan wata 29 ga Yuli, 2023 Daga Madakin Zazzau, Alhaji Muhammadu Munnir Ja’afaru, ya ajiye Mukaminsa na Hakimin Basawa, Sarkin Zazzau, Mai Martaba, Malam Ahmed Nuhu Bamalli. , CFR, LLD, Ya Gaggauta Amincewa da Naɗin Architect Haruna Abubakar Bamalli, Barde Kerrariyan Zazzau, Wanda Shine Hakimin Zangon Aya, a Matsayin sabon Hakimin Basawa,” kamar yadda Malam Aliyu ya bayyana.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
