Connect with us

News

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta rufe gidajen mai guda biyar

Published

on

Yan sanda a bakin aiki

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa mai kula da harkokin man fetur ta rufe gidajen Mai  guda biyar bisa laifin damfarar kwastomomi.

Advertisement

Shugaban Taskforce, Kanar Muhammad Alhassan (Rtd) ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya duba wasu gidajen mai a kananan hukumomin Kiyawa, Gumel, da Jahun.

Yarima Munir Ja’afaru, Ya Miƙa Takardar Murabus ɗinsa na Hakimin Basawa.  

Ya ce an duba ayyukan gidajen man ne domin tabbatar da sun bi ka’idojin da aka gindaya.

Advertisement

Alhassan ya bayyana cewa, Taskforce ta yi gargadin sama da gidajen mai talatin (30) tare da rufe biyar (5) saboda yin wasu ayyukan da ba su dace ba.

Ya ce kwamitin zai ci gaba da duba sauran gidajen mai tare da fallasa duk wani gidan mai da aka samu yana damfarar mitoci don rage masu mu’amala da su.

Advertisement

 

 

Advertisement

Daily Post

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending