Connect with us

News

Gwamnan Jahar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce Mako Mai Zuwa Za,a Fara Biyan Yan Fansho 

Published

on

Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

 

Gwamnan jahar kano Abba Kabir Yusuf ya ce an ware kimanin Naira biliyan 6 domin biyan ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya kimanin 5,500 hakkokin su.

Advertisement

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Asabar a Kano.

Za mu nuna wa duniya cewa Isra’ila ta aikata laifukan yaki: Shugaban Turkiyya

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa gwamnan tun bayan hawansa mulki, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda gwamnatin da ta shude ta mayar ta gaza biyan yan fansho hakkokin na garatiti wanda ya kai sama da Naira biliyan 40.

Advertisement

Gwamnan ya yi alkawarin biyan dukkanin wadanda suka gama aikin hakkokin su cikin Shekarun biyu masu zuwa .

Abba Kabir Yusuf ya ce an cimma matsayar ne a taron majalisar zartarwa na mako-mako a ranar Laraba.

Advertisement

A cewarsa, wadanda za su ci gajiyar kudaden da za’a biya za su kasance ne wadanda suka yi ritaya a matakin albashi ma kasa-kasa, wadanda kudaden su ka Kai Naira miliyan daya zuwa kasa, inda ya jaddada cewa kudaden da za’a iya yan fanshon ba bashi aka karɓo su ba .

 

Advertisement

Gwamnan ya ce ya damu matuka da halin da ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya suke shiga a jihar, bayan hidima da suka yiwa kano, amma gwamnatin da ta shude ta ki biyansu hakkokinsu.

“Muna da jerin sunayen wadanda zasu amfana, kuma muna da kudaden hannu, nan da mako mai zuwa za mu fara biyan ba tare da bata lokaci ba.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending