Connect with us

News

NLC, TUC Sun Yabawa Gwamna Sani kan sakin naira biliyan 3.1 Ga ‘Yan Fansho a Kaduna

Published

on

Gwamnan Jihar Sanata Uba Sani

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Shugabanin kungiyoyin kwadagon kasa NLC da TUC da kungiyar ‘yan fansho ta Kasa NUP a jihar Kaduna sun yabawa gwamnan jihar Sanata Uba Sani kan sakin naira biliyan 3.1 domin biyan kudin yan Fansho.

A wasu wasiku daban-daban da Shugaban NLC, Ayuba Suleiman, Shugaban TUC, da NUP suka sanya wa hannu, kungiyoyin kwadagon sun godewa Gwamna Sani da gwamnatin jihar Kaduna kan yadda aka sako kudaden ga ‘yan fansho a kan lokaci duk da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Advertisement

Gobara ta kone sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Borno

A cewar kungiyoyin, biyan kudin gratuti ga ’yan fansho zai zama wani gaggawar shiga tsakani wanda zai rage radadin wadanda suka yi ritaya da kuma iyalan abokan aikinsu da suka rasu da suka yi aiki a ma’aikatan gwamnatin jihar Kaduna.

Kungiyoyin kwadagon a yayin da suke yin alkawarin bayar da goyon bayansu ga gwamnatin da Gwamna Sani ke jagoranta, sun yi kira ga kundin tsarin mulki na hukumar fansho ta jihar Kaduna da ta tabbatar da gaskiya cikin sashe na 20 na dokar sake fasalin fansho ta jihar, 2020.

Advertisement

 

Channels

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending