News
Majalisar dokokin Jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar dokokin Jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi na ‘YanKwashi ya Birniwa da kuma Gumel bisa zargin su da rashin da’a.
Shugaban kwamitin kananan hukumomi a majalisar Honarabul Aminu Zakari shine ya tabbatarwa wakilin mu na Dutse hakan.
NLC, TUC Sun Yabawa Gwamna Sani kan sakin naira biliyan 3.1 Ga ‘Yan Fansho a Kaduna
Yace dakatarwar ta biyo bayan tafiya kasar Rwanda da shugabannin kananan hukumomin uku sukayi, da kin halartar gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 da gwamna yayi a gaban majalisar.
Alh Aminu Zakari ya bayyana cewa an kafa kwamiti karkashi jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar honarabul Lawan Muhammad Dansure domin yayi bincike kan dalilin da ya hana ciyamomin zuwa gabatar da kasafin kudin duk da mahimmacin sa ga jiha.
Ya kuma kara da cewa shugabannin kananan hukumomi 9 sun tafiya amma shida daga cikin su sun dawo domin halartar gabatar da kasafin kudin, yayinda ragowar ukun suka ki dawowa.
