Connect with us

News

Kungiyoyin Kwadago Sun Sanar Da Janye Yajin Aikinsu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gamayyar kungiyoyin kwadago a Najeriya na NLC da TUC sun sanar da janye yajin aikin da suka fara ranar Talata.

Advertisement

Kungiyoyin dau sun tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani ne ranar Talatar domin nuna bacin ransu da dukan da aka yi wa Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero a Jihar Imo a kwanakin baya.

Majalisar dokokin Jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi

A lokacin dai Ajaero ya jagoranci ma’aikatan Imo domin wata zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan wasu manufofin Gwamnan Jihar, Hope Uzodinma.

Advertisement

Sai dai daga bisani wasu ’yan daba da ake zargin magoya bayan Gwamnan ne suka lakada masa duka sannan ’yan sanda suka tsare shi.

Hakan dai ya janyo fushin kungiyoyin kwadagon, wadanda suka tsunduma yajin aiki a ranar Talata don nuna goyon bayansu gare shi.

Advertisement

Daily Trust ta rawaito cewa Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya sa labule da kungiyoyin a ranar Laraba, a kan yajin aikin, inda ya ce tuni ma aka kama mutum biyu da ake zargi da duka Ajaeron.

Wakilinmu ya jiyo daga wasu jiga-jigan ’yan kwadago yayin taronsu na musamman suna cewa sun amince da daukar matakin ne bayan nazarin dukkan alkawuran da Ribadun ya yi musu.

Advertisement

Shi ma Sakataren kungiyar ma’aikatan gwamnati ta AUPCTRE), Kwamared Sikiru Waheed, shi ma ya tabbatar da labarin ga ’yan jarida.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending