News
Rundunar ‘Yan Sanda Sun Kama Wadda Ake Zargi Da Kisan Malamar Jami’a A Minna
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta damke wata ‘yar aikin gida mai suna Joy Afekafe ‘yar shekara 14 da haihuwa bisa zargin kashe mataimakiyar Farfesa Funmilola Adefolalu na Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke FUT a Minna a Jihar Neja.
An kama ta ne a unguwar Gbeganu da ke Minna, babban birnin jihar a ranar Litinin bayan binciken share fage na ‘yan sanda.
Gwamnonin PDP za su tattauna don sulhunta Gwamna Fubara da Wike
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, PPRO, na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewa wadda ake zargin ta amsa laifin hada baki da wasu abokanta maza biyu don aiwatar da kisan.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa yayin da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa ta yi aiki a matsayin yar aikin gidan marigayiyar na tsawon makonni uku amma anki a sallame ta ne saboda munanan ayyukan da ta yi a gidan.
A cewar sanarwar ta ce bayan an sallame ta, ta hadu da abokan karatunta da ake kira Walex da Smart, ta ba su labarin irin wahalar da ta sha tare da hada baki wajen kai wa malamar hari a gidanta.
Sanarwar ta ce sun je gidan ne a ranar 28 ga Oktoba, 2023, da karfe 4:00, tare da babur, inda ta fito a bakin gate sai ta bude musu gate suka shiga daga cikin gidan.
Sanarwar ta bayyana cewa daga baya Walex da Smart ne suka shiga, suka lakada wa marigayiyar duka sannan suka daba mata wuka da Walex ya kawo, yayin da Smart ya dauko wata wuka daga kicin ya caka mata wuka da dama.
A wani labarin kuma Gwamnonin PDP za su tattauna don sulhunta Gwamna Fubara da Wike
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
