Connect with us

News

Wata babbar Kotu ta umarci EFCC ta saki Emefiele ko ta gurfanar da shi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Mai shari’a Adegbola Adeniyi na babbar kotun birnin tarayya, ya bayar da umarnin a gaggauta sakin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ba tare da wani sharaɗi ba.

Wannan umarni ya zo ne a matsayin martani ga wata buƙatar gaggawa da Emefiele ya shigar, inda ya buƙaci a sake shi daga hannun Hukumar Yaƙi da cin Hanci da Rashawa Ta Najeriya (EFCC).

Kotu Ta Tsare Tsohon Shugaban KASCO A Gidan Yari Kan N3.2bn

Kotun ta umurci hukumar EFCC ta gurfanar da Emefiele a gaban kotu a ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba, 2023, wadda ita ce ranar da aka sanya da za a ci gaba da sauraron ƙarar da aka shigar, tare da yiwuwar kotu ta bayar da belinsa.

 

Advertisement

Emefiele dai ya shigar da buƙatar gaggawar ne a gaban kotu, inda ya buƙaci a tilasta wa hukumar EFCC ta sake shi daga gidan yari, har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan shari’ar da ya dace.

 

A ranar 9 ga watan Yuni ne dai shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele daga mukaminsa na shugaban babban bankin ƙasar

A wani labarin kuma Kotu Ta Tsare Tsohon Shugaban KASCO A Gidan Yari Kan N3.2bn

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending