Connect with us

News

Kotu Ta Tsare Tsohon Shugaban KASCO A Gidan Yari Kan N3.2bn

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Babbar Kotun Jihar Kano ta tsare tsohon Manajan-Daraktan Hukumar Kayayyakin Noma ta jihar (KASCO), Bala Muhammad Inuwa kan zargin satar Naira biliyan 3.2 daga asusun gwamnatin jihar.

Kotun ta ba da umarnin tsare shi ne a yayin ci gaba da sauraron shari’ar da ake zargin shi da dansa aikata laifuka 10 da suka danganci raba wa mukarrabansu Naira biliyan 3.2.

Sojoji Sun Yi Ruwan Wuta Kan ‘Yan Ta’addan da Suka Halaka Mutum 160 A Borno Da Yobe

Lauyan gwamnatin jihar, Zaharadeen Hamisu Kofar Mata, ya ce masu gabatar da kara sun mika wa kotun gamsassun hujjoji da shaidun da ya kamata, domin ta hukunta wadanda aka zargin.

Ya kuma kalubalanci bukatar lauyan wadanda ake kara, Farfesa Nasiru Adamu Aliyu, na nema beli.

Advertisement

Sai dai a martaninsa, Farfesa Nasiru ya ce, lauyan masu kara da neman a hukunta wadanda ake zargi ba tare an bi tsarin da ya dace ba, don haka ya bukaci kotu kada ta biye wa bangaren masu kara.

Bayan sauraron bangarorin ne alkalin kotun, Mai Shari’a Hafsat Sani Yahya ta bayyana cewa masu kara sun gabatar da wadatattun shaidu da hujjoji da za a iya ci gaba da shari’ar.

Don haka ta bukaci lauyan wanda ake kara ya kara shigar da bukatar neman beli, wanda ta ce za ta karba.

Daga nan ta dage zaman zuwa ranar 6 ga watan Disamba, 2023.

A wani labarin kuma Sojoji Sun Yi Ruwan Wuta Kan ‘Yan Ta’addan da Suka Halaka Mutum 160 A Borno Da Yobe

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending