Connect with us

News

Sojoji Sun Yi Ruwan Wuta Kan ‘Yan Ta’addan da Suka Halaka Mutum 160 A Borno Da Yobe

Published

on

DAGA UASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Sojoji sun yi nasarar kashe ‘yan ta’addar kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad da aka fi sani da Boko Haram su kimanin 160 tare da lalata maboyarsu sakamakon wani hari da rundunar sojojin saman Nijeriya suka kai musu ta jiragen yaki a jihohin Borno da Yobe.

Rundunar sojin sama ta Operation HADIN KAI ce ta kai wannan harin kan maboyarsu biyu da aka gano a ranar Alhamis, 2 ga watan Nuwamba, 2023.

Advertisement

Ma’aikatan wutar lantarki sun umarci mambobinsu su janye ayyukansu bayan jikata shugaban NLC

Leadership ta rawaito cewa Maboyar ‘yan ta’addar da harin sojojin saman ya ritsa da su sun hada da maboyarsu ta yankin Bulabulin daura da kogin Komadugu-Yobe kusa da Geidam a jihar Yobe.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma kwararre kan yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana cewa harin da aka kai a yankin Bulabulin daura da kogin Komadugu-Yobe an kai ne kan babbar cibiyar Boko Haram, inda ‘yan ta’addar daga baya suka hada kai suke gudanar da ayyukansu a wurin.

Advertisement

A wani labarin kuma Ma’aikatan wutar lantarki sun umarci mambobinsu su janye ayyukansu bayan jikata shugaban NLC

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending