News
Jami’an NDLEA Sun Kama Hodar Iblis Da A Ka Boye A Cikin Turmi Za A Kai China
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wani ƙunshin hodar iblis da aka ɓoye cikin wani turmin katako na gargajiya da ake shirin tura wa ƙasar China.
Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi.
Majalisar Dokokin Kano Ta Haramta Makarantu Masu Zaman Kansu Ƙara Kuɗin Makaranta Sama Da Kashi 10
A cewarsa, jami’an NDLEA sun gano gram 250 na hodar iblis da aka ɓoye cikin turmin katakon, wanda aka saba amfani da shi wajen daka hatsi da sauran abinci, domin kauce wa binciken jami’an tsaro.
Babafemi ya ce binciken ya nuna cewa an shirya jigilar ƙunshin miyagun ƙwayoyin ne zuwa ƙasar China.
Ya ƙara da cewa jami’an hukumar sun kuma kama wani ƙarin ƙunshin hodar iblis da aka nufa da kai wa ƙasar Italiya, inda aka ɓoye ta a ƙasan wata jaka da aka ƙera ta musamman, sannan aka rufe ta da kayan yadin lace domin ɓatar da zato.
Kakakin NDLEA ya ce nasarar ta sake nuna yadda masu safarar miyagun ƙwayoyi ke ci gaba da amfani da sabbin dabarun ɓoye haramtattun kayayyakinsu, amma jami’an hukumar na ci gaba da bankado su tare da dakile yunƙurin safarar miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasashen waje.
