Connect with us

News

Manufofin Gwamnatin Shugaba Tinubu Sun Jefa Yan Najeriya Cikin Matsin Rayuwa ‎ ‎ ‎—Seyi Makinde

Published

on

IMG 20260804 000818 256

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APM kuma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce tsare-tsaren tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Tinubu ta zo da shi sun jefa ƴan ƙasa cikin matsi tare da tsadar rayuwa a Najeriya.

‎Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a birnin Abeokutan jihar Ogun, yayin ƙaddamar da ƴan takarar gwamna, majalisar dattijai, da ƴan majalisun dokokin jihar.

Mutum Miliyan 2 Na Ɗauke Da Cutar Hanta (Hepatitis) A Kano — KSACA

‎Gwamnan wanda ya samu wakilcin jagoran jam’iyyar, Babatunde Tijani, ya ce Najeriya na buƙatar a sake fasalin tattalin arziƙinta, tsaro da kuma shugabanci baki ɗaya.

‎Ya kuma ce tanade-tanaden tattalin arziƙin da ake da su a yanzu sun jefa ƴan ƙasar ne kawai cikin wani hali. Inda ya ce an janye tallafin man fetir da sakin naira ta nemowa kanta daraja ba tare da an yi duba na tsanaki wajen magance illar da hakan ke tattare da shi kan ƴan ƙasa ba.

‎Makinde ya ce kafin yanzu yan ƙasa na yin bacci idonsu a rufe, saboda sun san ba su da wata matsala, amman yanzu hakan ba zai yiwu ba. Inda ya ce dole ne gwamnati ta fifita buƙatun ƴan ƙasa fiye da komai.

Advertisement

‎Gwamnan ya ce da yawan mutane yanzu ba sa iya cin abinci sau uku a rana, baya da tsadar man fetir da ake fama da ita. Inda ya ce babu wata ƙasa mai hankali da za ta aiwatar da irin waɗannan tsare-tsaren ba tare da yin duba da halin da al’umma za su shiga ba.

 

 

DAILY TRUST

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending