News
Wani Miji ya rasa ransa a kokarin sa na kare matar sa daga harin ‘yan daba
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ibrahim Ahmadu mai shekaru 25, mijin Amina ya rasa ransa a kokarin sa na kare matar sa daga harin ‘yan daba a garin Bazai da ke karamar hukumar Shira a jihar Bauchi.
Wadanda ake zargin, Awalu Idi mai shekaru 20 da kuma Habibu Buba mai shekaru 20 sun hadu da Amina a bakin titi a lokacin da suke dawowa daga taron Mauludi, inda suka bukaci mijin da ya damka musu matar, shi kuma yaki.
Mashako: Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano ya Gargadi Jama’a kan Shirya Taruka Barkatai
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce wadanda ake zargin sun yi yunkurin kwace matar daga hannun mijinta ‘Ibrahim Ahmadu’wanda ya rasa ransa sakamakon jayayya da yayi da su.
Ya kara da cewa, “Saboda haka, wadanda ake tuhumar sun hada karfi sukai masa dukan tsiya da sanduna wanda hakan ya sa yaji ciwo ta cikin sa.”
Wakil ya ce an yi gaggawar kai shi babban asibitin inda likita ya tabbatar da mutuwar sa.
Da suke ansa tambayoyi wadanda ake tuhumar sun ansa laifin su,Zuwa yanzu dai ana cigaba da gudanar da bincike ,yayin da aka gama za a gurfanar da su a gaban kuliya.
A wani labarin kuma Mashako: Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano ya Gargadi Jama’a kan Shirya Taruka Barkatai
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
