News
Rwanda Ta Bada Sanarwar Shiga Kasar Ba Tare da Biza Ba Ga ‘Yan Afirka
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya gabatar da shirin bulaguro zuwa kasar sa ba tare da biza ga daukacin ‘yan Afirka ba, lamarin da ya sa kasar Rwanda ta kasance kasa ta hudu a Afirka da ke yin hakan.
Shugaba Kagame ya ce babu kuskure game da hakan, kuma duk wani ba’afrike na iya hawa jirgi zuwa Rwanda a duk lokacin da ya ga dama kuma ba zai biya komai ba don shiga kasar.
Wani Miji ya rasa ransa a kokarin sa na kare matar sa daga harin ‘yan daba
Yanzu haka Rwanda ta hade da Seychelles, Gambia da Benin, kasashen Afirka da ke ba da izinin shiga ba tare da biza ba ga dukkan ‘yan Afirka.
A wannan makon, shugaban kasar Kenya William Ruto ya sanar da cewa kasar za ta kawo karshen bukatuwar biza ga dukkan masu ziyara a Afirka nan da shekarar 2024. Haka kuma kasashen Afirka da dama sun kulla yarjejeniya da kasashen biyu na tafiye-tafiye ba tare da biza ba, na baya-bayan nan sune kasar Ghana da Afirka ta Kudu, da Uganda da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
