Connect with us

News

Mayakan Houthi sun sha alwashin kai hari kan duk wani jirgin ruwa na Isra’ila

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Mai magana da yawun kungiyar Houthi ta Yemen, Yahya Sarea ya bayyana cewa kungiyar za ta kai hari ga duk wani jirgin ruwa na kamfanonin Isra’ila ko kuma yake dauke da tutar ta Isra’ila, kamar yadda kungiyar ta bayyana a shafinta na Telegram.

Trt Word ta ruwaito cewa Yahya Sarea ya bukaci duka kasashen duniya su janye mutanensu da ke aiki a ire-iren jiragen ruwan.

Advertisement

Rundunar Sojojin ruwa sun kama buhu 50 na tabar wiwi da kudinsu ya kai Naira miliyan 70

Mayakan na Houthi sun yi wannan barazanar ne a daidai lokacin da adadin mutanen da Isra’ilar ta kashe ya haura 13,300 wadanda akasarinsu yara ne kanana da mata.

A wani labarin kuma Rundunar Sojojin ruwa sun kama buhu 50 na tabar wiwi da kudinsu ya kai Naira miliyan 70

Advertisement

Hukumar Lafiya ta Duniya, (WHO) ta ce akwai marasa lafiya 291 da ke cikin tsananin jinya a asibitin al-Shifa da ke birnin Gaza, bayan a jiya ɗaruruwan Falasɗinawa sun fice daga asibitin a ƙafa.

Kashi biyu cikin uku na marasa lafiyar jarirai ne da ke cikin mawuyacin hali, kamar yadda WHO ɗin ta bayyana.

Advertisement

Daga cikin marasa lafiyar, WHO ta ce suna ɗauke da munanan raunukan karaya, da waɗanda aka yanke musu ƙafa ko hannu, da masu raunuka a kansu da kirji da raunukan da suka danganci cikin jiki.

Likitoci 25 ne suka rage a asibitin na al-Shifa.

Advertisement

A jiya ma’aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce akwai kimanin marasa lafiya 120 da suka rage a asibitin

Sai dai BBC ba ta iya tantance hakiƙanin waɗannan alƙaluma ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending