News
Rundunar Sojojin ruwa sun kama buhu 50 na tabar wiwi da kudinsu ya kai Naira miliyan 70
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya (FOB) a ranar Lahadi, a Badagry, dake Legas, ta kama buhunan tabar wiwi 50 da darajarsu ta kai Naira miliyan 70 daga unguwar Gbethrome.
A cewar Lt.Commander Kelly Umoru, jami’in kula da ayyuka na FOB, ma’aikatan ne suka kwashe kayan daga wani gini da ba a kammala ba kusa da bakin teku da misalin karfe 6:30 na safe.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kira al-Shifa da ‘sansanin mutuwa
Umoru ya ce jami’an sojin ruwa sun dauki matakin ne a matsayin martani ga wani rahoto da aka samu kan inda ake zargin masu fasa kwauri a yankin.
Daily Post ta ruwaito cewa a ranar 9 ga Nuwamba, 2023, Babban Jami’in Rundunar Sojojin Ruwa ta Yamma, Rear Admiral Mustapha Hussain ya kaddamar da wani aiki mai suna ‘Water Guard’ tare da umarnin Babban Hafsan Sojan Ruwa.
“FOB Badagry a ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba, yana aiki da sahihan bayanan inda ya kai hari Gbethrome kuma ya gano buhunan 50 na cannabis sativa da ake zargin an adana a wani gini da aka yi watsi da shi kusa da bakin teku.
“Kowace buhunan na dauke da buhunan kusan 200. Farashin kayayyakin ya kai Naira miliyan 70,” inji shi.
Idan dai za a iya tunawa, rundunar sojin ruwan Najeriya da ke yankin Badagry ta mika wa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA buhunan tabar wiwi guda 27 wanda darajarsu ta kai naira miliyan 35 a ranar 4 ga watan Oktoba.
Kwamandan rundunar ta FOB, Kyaftin Aiwuyor Adams-Aliu ya ce jami’an tsaro ne suka kwashe kayan a ranar 29 ga watan Satumba a bakin tekun Pako da ke Badagry.
Awani labarin kuma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kira al-Shifa da ‘sansanin mutuwa
Qatar na taka muhimmiyar rawa a yunƙurin tattaunawar sulhu don sakin Isra’ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.
Kawo yanzu ta shiga tattaunawa da ta kai ga sakin mutum huɗu, ciki har da Amurkawa biyu, ‘ya da mahaifiya, da kuma wasu tsofaffi mata ‘ya Isra’ila guda biyu.
Qatar – mai ɗimbin arzikin albarkatun iskar Gas da ke yankin Gulf – ta kasance mafakar manyan shugabannin siyasar Hamas, da ke da ofishi a birnin Doha, tun shekarar 2012, da shugabanta Ismail Haniyeh ke jagoranta.
A ofishin ne jami’an ƙungiyar ke zama da jami’an diplomasiyya daga ma’aikatar harkokin wajen Qatar domin tattauna yadda za a saki mutanen.
Tun da farko, firaminstan Qatar, Mohammed bin Abdulrahman al-Thani, ya shaida wa taron manema labarai cewa “‘yan matsaloli ƙalilan ne suka rage a kammala tattaunawar, idan aka kwatanta da manyan, “suna da wahala, sannan suna da saukin sha’ani.”
Sai dai har yanzu ba a ga ma’anar abinda yake nufi da ‘saukin kai’ ba.
