Uncategorized
AMURKA: An Kama ’Yar Najeriya Kan Zargin Yin Zaɓe Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Hukumomin Amurka sun kama wata ’yar Najeriya mai shekaru 56, Gladys Adaeze Okafor, bisa zargin yin rajistar zaɓe da kuma jefa ƙuri’a ba bisa ƙa’ida ba, duk da cewa ba ’yar ƙasar Amurka ba ce.
Okafor, wadda ke zaune a birnin Lynn na jihar Massachusetts, an gurfanar da ita kan zargin yin zaɓe ba bisa ƙa’ida ba a matsayin wadda ba ’yar ƙasar Amurka ba, a zaɓen tsakiyar wa’adin mulki na shekarar 2022 da kuma zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na 2024.
Dakarun Soji Sun Kubutar Da Mutane 31 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Jihohin Katsina Da Kebbi
A cewar takardun ƙarar, Okafor ’yar asalin Najeriya ce da aka haifa a Aba. An ce ta samu matsayin zama na dindindin a Amurka a watan Disamba na 2022, amma ba ta zama ’yar ƙasar Amurka ba, kuma ba ta nemi zama ’yar ƙasar ba.
Hukumomi sun zarge ta da yin rajistar zaɓe a watan Yulin 2022, inda ta sanya hannu a kan wata takarda tana tabbatar da cewa ita ’yar ƙasar Amurka ce. Daga bisani, an yi mata rajista a matsayin mai zaɓe, sannan ana zargin ta da jefa ƙuri’a a zaɓen tsakiyar wa’adin mulki na shekarar 2022.
Ana kuma zargin cewa a watan Oktoban 2023 ta sake cike wata takardar rajistar zaɓe, inda ta sake bayyana cewa ’yar ƙasar Amurka ce. Daga nan ne ake zargin ta da jefa ƙuri’a a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na 2024.
Idan aka same ta da laifi, dokar Amurka ta tanadi hukuncin da zai iya kaiwa shekara guda a gidan yari, shekara guda na kulawar shari’a bayan hukunci, da kuma tarar da za ta iya kaiwa dala 100,000. Haka kuma, hukumomi sun ce tana iya fuskantar yiwuwar korar ta daga Amurka bayan kammala duk wani hukuncin da kotu ta yanke.
Sai dai Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta jaddada cewa zarge-zargen da ke cikin takardar ƙarar ba su tabbatar da laifinta ba, kuma ana ɗaukarta a matsayin marar laifi har sai an tabbatar da laifinta a gaban kotu ba tare da wata shakka mai ma’ana ba.
