News
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kira al-Shifa da ‘sansanin mutuwa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana asibiti mafi girma a Gaza na Al-Shifa da cewa ya zama “sansanin mutuwa”, bayan ficewar ɗaruruwan mutane daga cikinsa
Tawagar haɗin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya ƙarƙashin jagrancin WHO ta samu ziyartar asibitin na tsawon sa’a guda bayan sojojin Isra’ila sun mamaye shi tare da tilasta kwashe marasa lafiya.
Tawagar ta ce ta ga hujjojin da ke nuna kai hare-haren makami da harbe-harben bindiga, tare da gano wani babban kabari a ƙofar shiga asibitin, wanda aka shaida musu cewa gawarwaki 80 aka binne a ciki.
A kwanakin baya-bayan nan ne sojojin Isra’ila suka kai samame asibitin, a wani ɓangare na abin da suka kira ”kai hari kan mayaƙan Hamas”.
Sai dai ba ta bayyana wata ƙwaƙƙwarar hujjar da za ta tabbatar da iƙirarin nata na cewa mayaƙan ƙungiyar na gudanar da ayyukansu a hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da ke ƙarƙashin asibitin.
A wani labarin kuma Gobara Ta Kone Dukiyar N4.6m A Kwara
Firamistan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya yi watsi da kiran dakatar da wuta tsakaninsa da Hamas.
Mista Netanyahu ya nanata cewa zai amince da tsagaita wuta na wucin gadi a matsayin musaya idan Hamas ta sako dukkan Isra’ilawan da ta ke yi garkuwa da su.
Ya ce ”mutane da dama a duniya sun yi kiran kar mu shiga Gaza, amma mun shiga. Sun ce kar mu shiga birnin Gaza, nan ma mun shiga, sun ce kar mu shiga Al-Shifa nan ma mun shiga. Dan haka babu batun tsagaita wutar dindindin sai dai ta wucin gadi”
Sai dai jaridar Washington Post, ta rawaito Isra’ila da Hamas da Amurka na gab da cimma matsayar sako mata da yaran.
