Connect with us

News

Gobara Ta Kone Dukiyar N4.6m A Kwara

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Gobara ta kone wani katafaren shaguna 8 tare da lalata wasu kadarori da aka kiyasta kimanin Naira miliyan 4.6 ranar Asabar a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Daily Trust ta ruwaito cewa Lamarin ya faru ne a Lamba 48 Basin Road, daura da Cocin CAC, karamar hukumar Ilorin ta Kudu.

Advertisement

WATA SHARI’A SAI A LAHIRA:  ‘Samun alƙalai nagari sai dace  – Akpata

Kakakin hukumar kashe gobara, Hassan Hakeem Adekunle, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce da isar ‘yan kwana-kwana ‘yan kwana-kwana sun ci karo da wata mummunar gobara da ta lakume shaguna 8 wanda ya yi sanadin lalata biyu daga cikinsu.

A cewarsa, an shawo kan gobarar da misalin karfe 2:20 na safe.

Advertisement

“Draktan hukumar kashe gobara, Yarima Falade John, ya shawarci jama’a da su rika kashe na’urorinsu a lokacin da ba a amfani da su.

A wani labarin kuma ‘Yan kato da gora sun kama mutanen da ke yin tsire da naman Kare

Advertisement

Firamistan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya yi watsi da kiran dakatar da wuta tsakaninsa da Hamas.

Mista Netanyahu ya nanata cewa zai amince da tsagaita wuta na wucin gadi a matsayin musaya idan Hamas ta sako dukkan Isra’ilawan da ta ke yi garkuwa da su.

Advertisement

Ya ce ”mutane da dama a duniya sun yi kiran kar mu shiga Gaza, amma mun shiga. Sun ce kar mu shiga birnin Gaza, nan ma mun shiga, sun ce kar mu shiga Al-Shifa nan ma mun shiga. Dan haka babu batun tsagaita wutar dindindin sai dai ta wucin gadi”

Sai dai jaridar Washington Post, ta rawaito Isra’ila da Hamas da Amurka na gab da cimma matsayar sako mata da yaran.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending