Connect with us

News

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Ba Wa Falasɗinawa Naira Miliyan 100

Published

on

Babban Malamin Musuluncin nan kuma Jagoran Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi Usman Bauchi

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

Babban Malamin Musuluncin nan kuma Jagoran Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi Usman Bauchi ya ba da gudunmawar Naira miliyan 100 domin tallafa wa mutanen Faladinu da Isra’ila ke yi mata yakin mamaya.

Advertisement

Sheikh Dahiru Bauchi ya ba da gudunmawar ce lokacin da aka karanta masa wasikar da Halifan Sheikh Ibrahim Nyass, Khalifa Sheikh Muhammadul Mahy Inyass ya rubuta wa dukkan almajiran Shehu Ibrahim cewa su taimaka a tara Dala miliyan daya da ya ce za a bai wa Falasdinawa da yaki ya tagayyara.

Daruruwan mata ne suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da korar da kotun daukaka kara ta yi wa Gwamna Abba

Advertisement

Takardar wadda Kakakin Shehu Mahiy a Nijeriya, Sayyadi Ibrahim Dahiru Bauchi ya kawo, an umurce shi ya hada kan dukkan almajiran Shehu Ibrahim su taimaka a hada wannan kudi.

 

Advertisement

Da yake kaddamar da asusun, Sheikh Dahiru Bauchi ya ba da gudunmawar Naira miliyan 100, inda ya bukaci jama’a su cika saura Naira miliyan 900 da ya rage.

 

Advertisement

 

Shehin ya ce, kada gwiwar kowa ta yi sanyi, kowa ya yi iyakacin kokarinsa don ganin ya ba da gudunmawa don a tara wannan kudi.

Advertisement

 

Da yake karin haske, Sayyadi Ibrahim Dahiru Bauchi ya ce, akalla kowane almajirin Shehu Ibrahim ya kamata ya ba da Dalar Amurka daya kwatankwacin Naira 1,200.

Advertisement

 

Sai ya yi kira ga dukkan Musulmi, musamman ’yan Tijjaniyya su yi kokarin bayar da nasu taimakon ta asusun banki na: SHEIKUL ISLAM ALHAJI IBRAHIM INYASS FOUNDATION, 0125407863 a WEMA BANK.

Advertisement

Sayyadi Ibrahim ya ce, abin da ya kawo wannan magana shi ne, Shehu Mahiy ya halarci taro ne a kasar Mauritaniya, inda aka fayyace halin da Falasdinawa suke ciki, sai ya yi alkawarin almajiran Shehu Ibrahim za su tallafa da Dalar Amurka miliyan daya sama da Naira miliyan dubu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending