News
Daruruwan mata ne suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da korar da kotun daukaka kara ta yi wa Gwamna Abba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Daruruwan mata ne suka gudanar da zanga-zanga zuwa rundunar ‘yan sandan jihar Kano domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda kotun daukaka kara ta soke zaben Abba Kabir Yusuf.
Matan wadanda ke dauke da alluna da kuma rera wakokin nuna goyon baya ga Mista Yusuf, sun ce suna nuna rashin amincewarsu da rashin adalcin da kotun daukaka kara ta yi wa mutanen jihar Kano.
Haramta Ayyukan Gidajen Gala Ya Janyo Cece-Kuce A Jihar Jigawa
Masu zanga-zangar wadanda suka fara tattakin ne daga gidan tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da ke hanyar Miller Road, sun je cikin lumana kai tsaye hedikwatar ‘yan sandan jihar Kano da ke Bompai domin mika takardar zanga-zangar.
Sai dai a kan hanyarsu ta zuwa yankin Bompai, tawagar jami’an ‘yan sanda da jami’an hukumar gidan gyaran hali ta Najeriya suka tare su, inda suka yi musu rakiya zuwa inda suke.
Matan wadanda akasarinsu sun sanya jajayen mayafi ne, sun taru ne a hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano, inda suka bukaci ganin kwamishinan ‘yan sanda Usaini Gumel.
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa Wannan dai shi ne karon farko a tarihin Kano da mata suka fito gaggarumar zanga-zanga kan tituna suna neman a yi wa dimokradiyya adalci tare da kare musu hakkinsu a zaben gwamna na ranar 18 ga Maris.
Daya daga cikin masu zanga-zangar lumana, Hajiya Rabi Hotoro, ta ce suna kan tituna domin nuna damuwarsu kan abin da ya faru a kotun daukaka kara a makon jiya.
Mun fita ne a yau saboda mun yi imani da dimokuradiyya da ‘yancin kai na bangaren shari’a, muna so mu yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi abin da ya kamata tare da barin ra’ayin jama’ar Kano ya tabbata.”
Kano dai ta fada cikin tashin hankali a siyasance biyo bayan cece-kucen da aka samu kan hukuncin da aka yanke na daukaka kara, inda aka sha banban da na magana da kuma a rubuce.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
