Connect with us

News

Sojoji sun kama  ‘yan bindiga 58 da ake zargi da yin garkuwa da mutane a jihar Filato da Kaduna.

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Dakarun Operation SAFE HAVEN (OPSH) da ke aiki da Operation HAKORIN DAMISA IV daga ranar 20 zuwa 27 ga watan Nuwamba a jihohin Kaduna da Filato, sun kama mutane 58 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da kisan kai da garkuwa da mutane, yayin da aka kashe dan ta’adda guda a yayin farmakin.

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da kuma hotuna da aka raba a ofishin rundunar sojojin Najeriya ta X a ranar Talata.

Advertisement

Daya daga cikin riƙaƙƙun ‘yan daba a jihar Kano, ya miƙa kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar.

Sojojin sun kuma ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su: Leah Redzak, Paulina Pwajock, da Dorathy Ajiji, wadanda aka yi garkuwa da su a kauyen Ndor da ke karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato. An ceto mutanen ne a kauyen Tenti da ke karamar hukumar Barkin Ladi na jihar.

Sanarwar ta kara da cewa, “An kama mutane tara da laifin yin garkuwa da mutane, biyar da laifin safarar makamai, tara da laifin kisan kai, hudu da barnata gonaki, 18 da ake zargin ‘yan fashi ne, 12 da laifin safarar miyagun kwayoyi, daya kuma na satar shanu.

Advertisement

“Bugu da kari, an ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su, an dakile hare-hare bakwai da aka kai kan al’ummomin da ba su da karfi, sannan kuma an amsa kiran gaggawa guda biyar. An kwato shanu 103 da raguna 40.”

“Baki daya, an kama mutane 58 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin makon da ya gabata yayin da aka kashe wani dan ta’adda.”

Advertisement

Kwamandan Operation SAFE HAVEN, Manjo Janar A.E. Abubakar, ya jaddada kudirin OPSH da sauran jami’an tsaro na ganin an kare masu bin doka da oda a jihohin Filato da Kudancin Kaduna da Bauchi ta kowace hanya ta halal.

 

Advertisement

Ya kuma umarci jama’a da su rika ba sojoji goyon bayan da ake bukata a kodayaushe, ya kuma ba su tabbacin za a gaggauta hukunta su da zarar an kammala binciken wadanda ake zargi a hannun OPSH.

 

Advertisement

Punch

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending