Connect with us

News

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun hallaka akalla mutane 11 masu saran itace a Borno 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun hallaka akalla mutane 11 masu saran itace a Karamar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno.

Rahotanni sun ce mayakan sun tare masu yin itacen ne a yammacin jiya Litinin a kauyen Damboa Iga da ke kusa da Bale, inda suka hallaka wasu daga cikin su.

Sojoji sun kama  ‘yan bindiga 58 da ake zargi da yin garkuwa da mutane a jihar Filato da Kaduna.

Wata majiya daga jami’an sa kai da ke aiki a yankin, ta ce an samu gawarwakin mutane 6 daga cikin wadanda ke aiki a wurin, bayan an daddatsa sassan jikinsu, kuma har anyi jana’izarsu kamar yadda addinin Islama ya tanada, yayin da 5 kuma suka bata.

Sai dai wata majiya da ta tsallake rijiya da baya, ta ce mutanen suna aiki ne a wajen da suke saran itace suna mayar da shi gawayi, lokacin da mayakan haye a kan rakuma suka afka musu, bayan sun musu kawanya.

Advertisement

Majiyar ta shaida wa wakilinmu cewar, lokacin da take gudu, mutanen sun bi ta, amma da yake ta fi su sanin yanayin hanyar, sai ta tsere musu.

Majiyar ta ce daga nan ta garzaya ta shaida wa jama’ar gari, inda suka yi gangami zuwa wurin, amma sai suka tarar da gawarwakin wadannan mutane guda 6 da aka daddatsa su, yayin da a yau Talata aka samu karin gawarwaki 5 na mutanen da suka bata.

Aminiya ta ruwaito cewa sojoji na can suna sintiri a yankin.

A Wani labarin kuma Sojoji sun kama  ‘yan bindiga 58 da ake zargi da yin garkuwa da mutane a jihar Filato da Kaduna.

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending