News
Majalisa Ta Ba Da Umarnin A Tsare Gwamnan CBN Da Akanta-Janar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar Tarayya ta ba da umarnin tsare Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardosa da Akanta-Janar na Kasa Oluwaoyin Madein.
Kwamitin Karbar Korafi na Majalisar ne ya ba da umarce tsare da wasu kamfanonin mai 15 kan kin amsa gayyatarsa domin amsa tambayoyi kan bangaren albarkatun man Najeriya,
Aminiya ta ruwaito cewa Kwamitiin majalisar ya ba da umarnin ne da murta daa baan samun korafi daga wani mai suna Fidelis Uzowanem a ranar Talata.
Sauran wadanda umarnin ya shafa su ne Kamfanin Kula da Zuba Jarin Mai na Kasa (NAPIM) da kamfanonin hakar danyen mai na Total da Shell da Agip da Pan Ocean Oil da Newcross E&P da kuma Frontier Oil.
Sauran su ne Ethiop Eastern Exploration and Production da Western Africa Exploration and Production.
A wani labarin kuma Dan Kwallo Ya Mutu Ana Tsaka Da Atisaye A Filin Wasa
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
