News
Yanzu Haka Masu Zanga Zanga Sun Nufi Majalisar Wakilan Najeriya domin nuna bacin ransu kan harin da sojoji Sukayi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Yanzu Haka Masu Zanga Zanga Sun Nufi Majalisar Wakilan Najeriya domin nuna bacin ransu kan harin da sojoji suka kaiwa mazauna garin Tudin Biri a jihar Kaduna inda mutane 120 suka rasu.
Dubban masu zanga-zanga sun fantsama titunan Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya, a wani mataki na nuna bacin rai kan kashe sama da mutane 120 da ke bikin maulidi Manzon Allah SAW a wani kauye da ke Tundun Biri na karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Masu zanga-zangar suna kira da a tsige ministocin tsaro tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.
Ga wasu hotunan zanga-zangar da wakilinmu na Abuja Mohammed Kabir Yusuf ya aiko mana.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
