Connect with us

News

Kwankwaso Ya Bayyana Takaici, Yayinda Amnesty Ke Cewa Wanda Suka Mutu  Yq Karu Zuwa 12O Sanadiyar Harin Bom Na Sojoji A Kaduna

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana bakin cikinsa kan harin bam da sojojin Najeriya suka kai a daren Ranar Lahadi a kauyen Tundun Biri dake jihar Kaduna, a yayin bikin Mauludi.

Kwankwaso ya bayyana harin da aka kira na kuskure a matsayin wani babban jigo na gazawar hukumomin tsaro, inda ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su biya diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da tabbatar da ganin an yi adalci.

Tinubu Da  Shattima Zasu Kashe Sama Da Billiyan 15 Wajen Tafiye-Tafiye A Shekarar 2024

Har ila yau, fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar da hukunta wadanda suka kai harin bam a kauyukan.

Arewa Radio ta ruwaito cewa adadin wadanda suka mutu a al’amarin ya karu zuwa 120 kamar yadda jami’an Amnesty International da suka ziyarci garuruwan da al’amarin ya shafa suka tabbatar da karuwar adadin wadanda suka mutu.

Advertisement

A wani labarin kuma Tinubu Da  Shattima Zasu Kashe Sama Da Billiyan 15 Wajen Tafiye-Tafiye A Shekarar 2024

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta saki wata sabuwar kididdiga da ke nuna ƙarancin harajin da ake sakawa a duniya kan barasa da lemukan zaki.

Bincike ya nuna akasarin ƙasashe ba sa amfani da haraji domin inganta lafiyar al’umma.

WHO ta kuma saki wani littai ƙunshe da bayanai kan harajin barasa.

A duniya, fiye da mutum miliyan biyu da rabi ne ke mutuwa sakamakon shan giya kowace shekara kuma sama da mutum miiyan takwas sakamakon rashin cin abinci mai inganta lafiya, saka haraji kan barasa da lemukan zaƙi zai rage yawan mace-macen da ake samu ta wannan ɓangare.

Rabin ƙasashen da ke saka haraji kan lemukan zaƙi suna sa haraji kan ruwa wanda WHO ba ta ba da shawarar haka ba.

Advertisement

Wani bincike da aka yi a 2017 ya nuna harajin da ke ƙara farashin barasa da kashi 50 cikin 100 zai rage mace-macen mutum miliyan 21 tare da samar da kuɗin shiga na dala triliyan 17.

Wannan ya yi dai-dai da jumullar kuɗaɗen shiga na ƙasashe takwas mafiya ƙarfin tattalin arziki a shekara ɗaya.

Hukumar lafiya ta duniya ta ba da shawarar a saka haraji kan dukkanin lemukan zaƙi da kuma barasa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending