Connect with us

News

Kotun Ƙoli: APC Da NNPP Sun Ƙulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Jihar  Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Jam’iyyun APC da NNPP a Kano sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a kan hukuncin da Kotun Ƙoli za ta yanke kan zaben gwamnan jihar.

Advertisement

Shugabannin jam’iyyun sun kulla yarjejeniyar ne a hedikwatar rundunar ’yan sandan jihar Kano a gaban kwamitin shugabannin hukumomin tsaro.

Hakkokin Talaka Da Suka Wajaba A Kan Shugabanni  -Malm Jafar 

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Usaini Muhammad Gumel, ya ce shugabannin jam’iyyun sun sabunta alkawarinsu na tabbatar da zaman lafiya a lokacin da kotu ta sanar da hukuncin da ta yanke da kuma a yayin bikin murnar nasara.

Advertisement

Ya ce taron ya tattauna kan wasu miyagun ’yan siyasa da ke yunkurin haɗawa tashin hankali a jihar, sannan ya yaba wa shugabannin APC da NNPP kan yadd tsayuwarsu a karo na bisa alkawarin da suka dauka da farko na zaman lafiya.

Usaini Gumel ya ce taron ya kuma tattauna kan matsalar shugabanci a cikin jam’iyyun biyu a wasu kananan hukumomin jihar.

Advertisement

A wani labarin kuma Hakkokin Talaka Da Suka Wajaba A Kan Shugabanni  -Malm Jafar 

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending