Labarai
Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Laifin Kashe Abokinsa Akan naira ₦100

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babbar kotun jihar Zamfara ta yanke wa wani mai suna Anas Dahiru hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe abokinsa kan kudi naira 100.
An gurfanar da Dahiru kotu ne a watan Yunin 2017 bisa zarginsa da kashe abokinsa, mai suna Shamu Ibrahim, ta hanyar cika masa wuka a lokacin da suke fada da juna kan kudi Naira 100.
Kotun Ƙoli: APC Da NNPP Sun Ƙulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Jihar Kano
Sawaba Fm ta ruwaito cewa Da yake karanta hukuncin, alkalin kotun, Mai shari’a Mukhtar Yusha’u, ya ce wanda ake zargin Anas Dahiru dake Unguwar Dallatu a Gusau babban birnin jihar, an gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar 2017 bisa zargin kashe abokinsa, Shamsu Ibrahim, da wuka akan rigimar kudi naira 100 kacal.
Yusha’u ya ce kotun ta saurari bangarorin biyu bayan haka ne kotun ta sami Anas da laifin kashe abokinsa.
A wani labarin kuma, alkalin kotun ya kuma yankewa wani mai suna Sadiku Abubakar hukunci bisa laifin yunkurin yin fashi da makami a karamar hukumar Bungudu.
An yankewa Sadiqu hukuncin ne bayan yunkurin yiwa wani dan kasuwa a kauyen Runji dake karamar hukumar Bungudu fashi da makami inda daga bisani aka damke dan fashin tare da mika shi ga ‘yan sanda.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
