News
Hukumar Hana Fataucin Mutane Ta Kasa Ta Ceto Tare Da Karbar Mutane 21,181 Da Aka Yi Fataucin Su
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar hana fataucin mutane ta kasa ta ceto tare da karbar mutane dubu 21 da 181 da aka yi fataucin su cikin shekaru 20.
Darakta Janar na Hukumar ta NAPTIP, Farfesa Fatima Waziri-Azi, ta bayyana hakan a lokacin data bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin jin dadin jama’a yayin kare kasafin kudin 2024.
Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Laifin Kashe Abokinsa Akan naira ₦100
Ta ce hukumar za ta yi kokarin tallafa wa wadanda abin ya shafa matukar suna bukatar a tallafa musu, inda ta ce tsarin na bukatar lokaci da kuma kudade.
Ta bayyana cewa hukumar ta NAPTIP tana bada tallafi domin gyara rayuwar wadanda abin ya shafa kamar yanda Sawaba radiyo ta ruwaito
Waziri-Azi ta bayyana cewa, a shekarar 2022, hukumar ta NAPTIP ta ceto tare da karbar mutane dubu 2 da 748 wadanda aka yi safarar su. Ta kara da cewa, “Daga watan Janairu zuwa Nuwamba 2023, hukumar ta ceto tare da karbar mutane dubu 2 da 200 da aka yi safararsu.
A wani labarin kuma Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Laifin Kashe Abokinsa Akan naira ₦100
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
