Connect with us

News

Abin Da Dahiru Bauchi Ya Ce Kan Sauya Sunan Kauyen Tudun Biri

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Shahararren malamin Musulunci kuma jagoran Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce sauya sunan gari abu ne da ya shafi al’ummar garin, idan kuma mutanen Tudun Biri suka zabi sauya sunan garinsu zuwa Tudun Maulidi, ya fi.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wannan kalami ne a ranar Asabar lokacin da aka tambaye shi cewa ko da gaske ne ya sauya wa garin suna zuwa Tudun Maulidi daga Tudun Biri.

Advertisement

Hukumar Hana Fataucin Mutane Ta Kasa Ta Ceto Tare Da Karbar Mutane 21,181 Da Aka Yi Fataucin Su

Sai ya ce “Idan mutanen garin suna so sai su sauya wa garin nasu suna zuwa Tudun Maulidi, ya fi.

“Saboda shi biri halinsa barna ne, Maulidi kuwa tuna tarihi ne na rayuwar Manzon Allah Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallama.”

Advertisement

Sai malamin ya yi addu’ar samun rahama ga wadanda harin bom din da jirgin soja ya jefa a wurin Mauludi a garin ya shafa.

Ya kuma yi addu’ar samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka a harin da kuma na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Advertisement

Tun lokacin da al’amarin ya faru dai malamin mai shekaru kusan 100 a duniya ya roki Gwamnatin Tarayya da ta binciko musabbabin faruwar hakan, kuma ta biya diyyan ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka sami raunuka.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Juma’a ne wasu suka rika sanya bayanai a intanet cewa malamin ya sauya wa garin suna zuwa Tudun Maulidi daga Tudun Biri.

Advertisement

Hadiman shehin da wakilin Aminiya ya zanta da su suka batun sauya sunan gari lamari ne na mutanen garin da mahukunta.

Amma babu laifi idan aka ba da shawara, suka karaba kuma suka sauya, domin yin haka zai sa a rika tuna wannan waki’a da ta sami mutanen garin lokacin da suke bukin Maulidi.

Advertisement

A wani labarin kuma Hukumar Hana Fataucin Mutane Ta Kasa Ta Ceto Tare Da Karbar Mutane 21,181 Da Aka Yi Fataucin Su

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending