News
Zarge-Zargen Muzanta Marasa Karfi A Bangaren Shari’a Sun Girgiza Al’ummar Jihar Kano, Rashin Adalci, Bangaranci Ko Amfani Da Iko?
...Korafin Tsare Yarinya Ta Hanyar Nuna Bangaranci Na Shirin Jefa Alkalin Hisba Cikin Tsaka Mai Wuya
KANO – Zarge-zargen rashin adalci da nuna son rai sun mamaye al’umma bayan bullar korafe-korafen da ke alakanta wani Alkalin Hukumar Hisba, Sani Tanimu, da abin da masu korafi suka bayyana a matsayin tauye hakkin wata yarinya marar gata.
Lamarin ya janyo cece-kuce, inda jama’a ke kira ga mahukunta su gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.
NDLEA Sun Cafke Mutane 73 Masu Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Kano
Rahotanni sun nuna cewa tunda farko rikici ne ya barke tsakanin wasu mata biyu, lamarin da ya kai ga shigar da maganar hannun jami’an tsaro. Sai dai duk da cewa bangarorin da abin ya shafa sun nuna alamun sasantawa, saidai wani mutum mai kumbar Susa ya daddage sai an ci gaba da shari’ar tare da daukar matakan da suka fi tsauri kan daya daga cikin bangarorin.
Jaridar Alfijir Labarai ta rawaito cewar masu korafi sun yi zargin cewa wani tsohon alkali mai suna Idris Yahya, wanda aka fi sani da “Mai Hannu Ɗaya”, ya taka rawa wajen yadda aka tafiyar da shari’ar. Sun ce tun kafin a gurfanar da yarinyar a gaban kotu an riga an tsara yadda za a tabbatar an tsare ta, lamarin da ya sa ake zargin cewa an yi amfani da dangantaka da kusanci wajen karkatar da akalar adalci.
A cewar bayanan da suka fito daga iyalan yarinyar, an kai ta gidan gyaran hali tun bayan gurfanar da ita a kotun Hisba duk da karancin shekarunta. An ce duk kokarin da aka yi na neman a ba ita beli, amma lamarin ya gagari kundila, yayin da alkalin ya ci gaba da kin amincewa da bukatar, abin da ya kara jefa iyalanta cikin damuwa da tashin hankali.
Bayan dawowar kotu daga hutun karshen mako, an sake mayar da yarinyar gidan gyaran hali, inda ta kara kwashe wasu kwanaki a tsare kafin daga bisani aka samu damar fitar da ita da beli. Wannan mataki ne ya kara fusata iyalanta, wadanda ke ganin cewa an nuna wariya da tsanani fiye da yadda yanayin rikicin ya kamata ya haifar.
Masu bibiyar harkokin shari’a sun bayyana cewa idan har wadannan zarge-zarge suka tabbata, to lamarin na nuna wani mummunan yanayi da ke iya rusa amincewar jama’a ga tsarin adalci. Sun ce babu abin da ya fi cutar da al’umma kamar ganin cewa mai karfi na iya rinjayar hukunci yayin da marar gata ke zama wanda ake danniya a kansa.
Har ila yau, wasu na ganin cewa wannan batu ya wuce rikicin mata kawai, domin ya shafi mutuncin hukumomin da aka dorawa alhakin kare hakkokin jama’a. A cewarsu, duk lokacin da aka samu zargin cewa ana hada baki da masu fada a ji wajen muzanta talaka, wajibi ne hukumomi su fito su tabbatar da gaskiya domin kawar da duk wata shakka.
Masu sharhi kan lamuran shari’a sun bukaci Gwamnan Jihar Kano da mahukuntan bangaren shari’a da su bude cikakken bincike kan lamarin. Domin jama’a na son a gano ko an bi ka’idojin doka yadda ya kamata ko kuma akwai wasu hannaye da suka yi tasiri wajen tsawaita tsare yarinyar fiye da yadda doka da adalci suka tanada.
Masu korafi sun jaddada cewa idan gwamnati ta yi shiru a kan irin wannan zargi, hakan zai kara karfafa tunanin cewa talaka ba shi da gata a gaban wasu masu iko. Sun ce lokaci ya yi da za a tabbatar wa al’umma cewa adalci ba na masu kudi da masu fada a ji kadai ba ne, kuma duk wanda aka samu da laifin karkatar da gaskiya ko amfani da matsayinsa wajen zaluntar marasa karfi dole ne ya fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
