News
NDLEA Sun Cafke Mutane 73 Masu Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Kano
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta kama mutane 73 da ake zargi da hannu a harkokin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi tare da ƙwace nau’o’in miyagun ƙwayoyi daban-daban a wani samame na musamman da ta gudanar a sassan jihar.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na NDLEA a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
A cewar sanarwar, Kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Dahiru Yahaya-Lawal, ya ce an gudanar da samamen ne a ranar 10 ga watan Yuni ƙarƙashin shirin “Operation Sharar Mafaka”, wanda ke da nufin kawar da wuraren da ake amfani da su wajen safarawa da shan miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.
Ya ce jami’an hukumar sun kai farmaki a wasu fitattun wuraren da ake zargin ana gudanar da harkokin miyagun ƙwayoyi, ciki har da Filin Mahaha, Cibiyar Matasa ta Sani Abacha da kuma wasu sassa na yankin Sheka.
Yahaya-Lawal ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna yawaitar ayyukan laifi da shaye-shaye a wuraren da abin ya shafa.
“Mun samu nasarar kama mutane 73 da ake zargi tare da ƙwace miyagun ƙwayoyi daban-daban, ciki har da tabar wiwi (Cannabis Sativa), Diazepam, Pregabalin, Exol-5 da wani sinadari da aka fi sani da ‘Suck and Die’, baya ga wasu kayan da ake amfani da su wajen safarawa da amfani da miyagun ƙwayoyi,” in ji shi.
Kwamandan ya ce hukumar za ta ci gaba da amfani da dabarar “rushewa da mamaye wuraren laifi” domin hana masu safarawa da amfani da miyagun ƙwayoyi samun mafaka a jihar.
