News
Majalisar Dattija Ta Yi Amai Ta Lashe Game Da Kiran Kamo Mele Kyari
Majalisar Dattijan Najeriya ta yi amai ta lashe game da kiran jami’an tsaro su kamo tsohon shugaban kamfanin mai na ƙasar Mele Kyari sakamakon ƙin bayyana da yayi gaban Majalisar don yin ƙarin haske game da ɓatan wasu kuɗade da yawansu ya kai Naira Triliyan 210, a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023.
Wannan na zuwa ne bayan da Kyari ya ƙi mutunta gayyatar da Majalisar ta yi masa a lokuta da dama, musamman bayan buƙatar hakan daga ofishin mai binciken kuɗi na gwamnatin tarayyar ƙasar.
Yayin da yake jawabi, shugaban kwamitin man fetur, Adams Ohiomole ya yayi wannan kira, yana mai umartar jami’an tsaro da su kamo Mele Kyari ko a mace ko a raye.
Ko da yake ƙalubalantar wannan kira a gaban kwamitin, babban jami’in da ke kula da harkokin kuɗi na kamfanin Umar Ajiya Isa, ya musanta batun ɓatan kuɗaɗen.
To sai dai tun bayan wannan kira, an samu cece-kuce da mayar da martani game da wannan kira yayinda wasu ke ganin yayi zafi a buƙaci kama Mr Kyari ko a mace ko a raye.
Wannan ce ta sanya yayin zaman Majalisar na yau shugabanta Godswill Akpabio yayi watsi da wancan kira na Oshiomole yana mai cewa babu yawun Majalisar cikin wannan kira a hukumace.
A cewar Akpabio, Oshiomole yayi wannan kira ne bisa raɗin kansa ba tare da sahalewar Majalisar ba, don haka wanna ra’ayinsa ne ba na Majalisa ba.
Akpabio ya kuma ce har yanzu Majalisar na bin hanyoyin da suka dace don ganin an sami maslaha da kuma cikakken bayani daga Mele Kyari kan waɗannan kuɗaɗe.
Sai dai Adams Ohiomole ya ce kiran nasa ya zama wajibi, ganin yadda ƙiri-ƙiri Kyari ke nuna rainuwa ga Majalisar, wannan kuma sannu a hankali yana zubar da ƙimar Majalisar don haka kamata yayi a ɗauki mataki mai zafi.
