News
Majalisar Matasan Arewa Ta Yabawa Majalisar Tarayya Kan Amincewa Da Dokar Kafa ’Yansandan Jihohi
Majalisar Matasan Arewa (Northern Youth Assembly – NYA) ta yaba wa Majalisar Dokoki ta Kasa bisa amincewa da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai bai wa jihohin Najeriya damar kafa rundunonin ’yan sanda na kansu.
A cikin wata sanarwa da Sakatare Janar na kungiyar, Dakta Abdulhafiz Garba, ya fitar, kungiyar ta bayyana matakin a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen sake fasalin tsarin tsaro da kuma magance matsalolin rashin tsaro da suka addabi sassan kasar nan.
Aƙalla Mutum 7,850 Sun Kamu Da cutar Kwalara A Borno
Sanarwar ta ce kuri’un amincewa 289 da ’yan majalisa suka kada, yayin da mutum hudu kacal suka nuna adawa, sun nuna cewa akwai cikakkiyar fahimta da goyon baya kan bukatar samar da sabbin hanyoyin inganta tsaro a Najeriya.
Kungiyar ta ce yankin Arewa ya dade yana fama da matsalolin tsaro da suka hada da hare-haren ’yan bindiga, garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, satar shanu, rikice-rikicen al’umma da sauran laifuffuka da suka janyo asarar rayuka da durkushewar harkokin tattalin arziki.
A cewar kungiyar, duk da kokarin da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ke yi, tsarin tsaro na kasa baki daya ya fuskanci kalubale sakamakon girman kasar, yawan jama’a da kuma bambancin matsalolin tsaro da ke addabar yankuna daban-daban.
Majalisar ta bayyana cewa kafa ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen kusantar jami’an tsaro da al’umma, tare da kara inganta tattara bayanan sirri da kuma dakile aikata laifuka tun kafin su afku.
Ta ce daya daga cikin manyan fa’idodin tsarin shi ne samun jami’an tsaro daga cikin al’ummomin da za su yi aiki a cikinsu, wadanda suka fi fahimtar harshe, al’adu da yanayin yankunansu.
Hakazalika, kungiyar ta ce tsarin zai taimaka wajen samar da dubban guraben ayyukan yi ga matasa, musamman a yankin Arewa, tare da rage zaman banza da ka iya jefa wasu cikin aikata laifuka.
Ta kara da cewa ingantaccen tsaro zai taimaka wajen jawo masu zuba jari, bunkasa noma da kasuwanci, da kuma farfado da tattalin arzikin yankunan karkara.
Majalisar Matasan Arewa ta kuma yi nuni da cewa kasashe irin su Amurka, Kanada, Ostiraliya da Jamus sun dade suna amfani da tsarin ’yan sanda na jihohi ko larduna, wanda ke aiki tare da hukumomin tsaro na kasa wajen tabbatar da doka da oda.
A karshe, kungiyar ta bayyana amincewar Majalisar Dokoki da kudirin a matsayin wani babban mataki na gina Najeriya mai zaman lafiya da tsaro, tana mai cewa hakan zai ba al’ummomin Arewa sabon fata na samun kariya, ci gaba da bunkasar tattalin arziki.
Kungiyar ta kuma tabbatar da ci gaba da goyon bayanta ga duk wata manufa da za ta inganta zaman lafiya, tsaro da hadin kan Najeriya.
