Connect with us

News

An Yanke Wani Matashi Hukuncin Kisa Kan Kashe Abokinsa Saboda Hula

Published

on

Rataya

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a titin Miller ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi mai suna Adamu Isma’ila Arzai, bisa samunsa da laifin kashe abokinsa Auwal Shehu Kabara, saboda gardama kan hula.

Lamarin ya faru ne a shekarar 2016, lokacin da fadan ya kaure tsakanin su a wata tafiya da suka yi domin fatauci zuwa Jihar Bauchi.

Advertisement

Ɓangaren Shari’ar Najeriya Cike Ya Ke da Baragurbin Alƙalai Masu Cin Hanci —El-Rufai

Rahotanni sun ce gardamar ta samo asali ne kan wata hular sanyi, inda daga karshe Adamu ya ciro wuka ya soka wa Auwal, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

A lokacin shari’ar, mai gabatar da kara, Wahida Isma’il, ta gabatar da shaidu biyar, yayin da wanda ake zargi ya kare kansa da bakinsa.

Advertisement

Bayan sauraron shari’ar, Mai Shari’a Muhammad Musa Karaye ya bayyana cewa kotu ta gamsu da hujjojin da aka gabatar, tare da tabbatar da cewa Adamu Isma’ila ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi.

Alkalin ya ce laifin ya sabawa sashe na 221 na kundin hukunta manyan laifuka na Jihar Kano, wanda ya tanadi hukuncin kisa.

Advertisement

Daga nan sai ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending