News
Gyara Bangaren Noma Zai Rage Rashin Aikin Yi Da Ta’addanci A Nijeriya- -Kashim Shettima
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ya bayyana juyin juya halin noma a matsayin mafita ga rashin zaman lafiya da talauci a kasar.
Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron karo na 13 na jami’ar Al-Hikmah da ke Ilorin, Kwara.
Kotun ƙolin Kasar Indiya za ta yanke hukunci kan kawo ƙarshen cin gashin kan yankin Kashmir
Da yake gabatar da jawabin mai taken: Maganin Kalubalen Tsaron Abinci ta Najeriya Ta Hanyar Hi-Tech: Matsayin Jami’o’in Najeriya,” Mataimakin Shugaban ya ce za a iya cimma nasarar tura fasahar samar da abinci ga al’ummar kasar nan.
Shettima ya jaddada mahimmancin ilimi da horarwa ga al’ummar kasar don samun cikakkiyar fa’ida daga fadada tasirin fasaha ta kowane bangare na rayuwar dan adam.
Sai dai lokacin da Najeriya ta fara tunanin kwarin guiwa game da kawo sauyi a harkar noma, sarrafawa, da kuma tabbatar da dorewar abinci, za ta iya gano sassan kadarorin noma na kasar da za su iya cin gajiyar amfani da fasahar zamani.
Makomar Najeriya za ta iya tabbatar da juyin juya halin noma ta hanyar tunani da jajircewar jagoranci, ingantaccen yanayi da kwanciyar hankali, da ingantaccen tsarin ilimi wanda ba zai rage iyakar ‘yan kasa zuwa sama kadai ba.
A wani labarin kuma Kotun ƙolin Kasar Indiya za ta yanke hukunci kan kawo ƙarshen cin gashin kan yankin Kashmir
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
