News
Kotun ƙolin Kasar Indiya za ta yanke hukunci kan kawo ƙarshen cin gashin kan yankin Kashmir
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kotun ƙolin kasar Indiya za ta yanke hukunci kan ƙarar da ke ƙalubalantar matakin gwamnatin ƙasar na shekaru huɗu da suka gabata kan kawo ƙarshen cin gashin kan yankin Kashmir.
An tsaurara matakan tsaro a yankin gabanin sauraron koken.
Kashmir shi ne kaɗai yankin da ya kasance musulmi sun fi rinjaye a Indiya, kuma kafin shekaru huɗu da suka wuce yankin na da damar samar da kundin tsarin mulki da yin dokokisa.
An dai haramtawa Indiyawa daga wajen Kashmir sayen duk wasu abubuwa a yankin.
A shekarar 2019, gwamnatin jam’iyyar BJP a Indiya ta ƙwace wannan damar tana mai cewa dole ne a haɗe yankin na Kashmir da Indiya.
Yunƙurin da ‘yan siyasa a Kashmir din suka ce ya saba ƙa’ida.
A wani labarin kuma Barcelona Ta Sha Kashi A Hannun Girona Da Ci 4-2
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
