Connect with us

News

Hukumar EFCC na tuhumar wasu ma’aurata da aikata damfarar Naira miliyan 410 A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da Aisha Malkohi da ka fo sani da Ummitah, Arab Money) da mijinta, Abubakar Mahmoud, bisa laifin damfarar Naira miliyan 410.5.

Hukumar ta gurfanar da Malkohi a gaban wata babbar kotun jihar Kano, yayin da mijinta ya arce, a cewar wata sanarwa da EFCC ta fitar ranar Litinin.

Matasan Kano sun yi zanga-zangar adawa da sace dalibai mata a Arewacin Najeriya

Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana a cikin sanarwar cewa wanda ake tuhuma an gurfanar da ita a gaban kotu bisa tuhume-tuhume biyar da suka shafi damfara na kudade har N410,518,000.

Premium Times ta ruwaito cewa ba ta aikata laifin ba a lokacin da aka karanta mata tuhume-tuhumen a gaban alkalin kotun, Aisha Mahmud.

Hukumar EFCC ta damke wadda ake zargin a Kano, biyo bayan karar da wasu masu shigar da kara guda biyu Farida Ibrahim da Ibrahim Mohammed Abdulrahman suka shigar, inda suke zargin ta hada baki da mijinta suka damfare su.

Advertisement

Masu ƙara sun ce ta damfare su ta hanyar amshe musu kuɗi da sunan za ta siyo musu motoci 64, gwalagwalai, da kayan wuta daga Saudiyya.

Bayan haka ne sai hukumar ta tsunduma farautar su da kuma bin diddigin abinda ya faru. EFCC ta gano cewa an jibga naira miliyan 410 a asusun wani kamfani mai suna Golden Grass, wanda mallakin wannan mata ce da mijinta.

Sannan an gano sun rika canja wa kuɗaɗen asusun ajiya ta hanyar rarraba su ita da mijinta zuwa wasu asusun ajiyan.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending